Kimanin dalar Amirka miliyan 150 ne sabon shirin ya kunsa a cewar ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Amirka, adadin da ya karu kan tallafin dala biliyan uku da digo takwas da kasar ta ambaci damka wa Ukraine don kare kanta daga mamayar Rasha.
Rahotanni sun ce an sake kwashe wasu karin fararen hula 50 a wannan Jumma'a da suka makale a kamfanin Azovstal na harhada karafuna a Marioupol, wanda dakarun Rasha suka yiwa kawanya, kana duk da yake Ukraine na zargin Rashar da karya yarjejeniyar tsagaita wuta don ficewa da fararen hula, ana sa ran ci gaba da ficewa da mata da yara da kuma gajiyayyu a wanna Asabar.
Yanzu hakan Rashar ta tsananta luguden wuta a yankin Donbass, kana ko a yammacin jiya ta kai wasu jerin hare-hare a yankin gabashin Severodonetsk da har yanzu ke hannun dakarun Ukraine. A wannan Asabar ake sa ran gabatar da taron kolin kasashen G7 masu karfin tattalin arzikin masana'antu na duniya, wanda zai ta'allaka kacokam kan batun yakin na Ukraine, kana kuma an gayyaci shugaba Zelensky da ya halarci taron da za a gudanar ta hanyar bidiyo.