Amirka ta soki lamirin Mali kan MINUSMA

Amirka ta soki lamirin Mali kan MINUSMA
Amirka ta yi kakkausar suka kan matakin gwamnatin mulkin soja a Mali ta dauka na takaita sarari ga rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya Minusma.

Jakadar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya Linda Thomas-Greenfield ta bayyana matakin a matsayin keta yarjejeniyar soja ta kasa da kasa da gwamnati Mali ta rattaba hannu a kai. A wannan Larabar ce dai kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kada kuri'ar sabonta wa'adin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Minusma a Mali, tare da tilasta wa gwamnatin kasar ba wa rundunar sarari, da ta aiwatar da bincike game da batun zargin taka hakin bani Adama kan fararen hula a yankin Moura da ke tsakiyar kasar, wanda kungiyoyin kasa da kasa ke tuhumar 'yan ta'adda da ma dakarun sojan Mali masu samun goyoyn bayan sojojin hayar Rasha Wagner da aikata wa, sai dai fadar mulki ta Bamako ta nuna rashin amincewa da matakin.


News Source:   DW (dw.com)