Hukuncin kisan shi ne irinsa na farko a shekaru da dama a Myanmar, kuma Amirka na daga cikin manyan kasashen duniya da ta soma sukar matakin aiwatar da hukuncin kisa kan mutanen hudu da suka hada da Phyo Zeya Thaw da Kyaw Min Yu da Hla Myo Aung da kuma Aung Thura Zawor.
A cikin sanarwar da fadar Washington ta fitar a dazun nan, ta yi Allah wadai da matakin da sojojin suka dauka na kashe wadanda suke hakilon ganin sun kare dimokradiyya a kasar, daga bisani Amirka ta kuma nemi gwamnatin da ke rike da mulkin da ta gaggauta sakin dubban fursunonin da ake tsare da su ba bisa ka'ida ba.
An dai kashe mutanen hudu ne bayan da gwamnatin ta ce, ta same su da laifuka na bayar da umarni da shirin aikata munanan laifukan ta'addanci. Daman bayan hambarar da gwamnatin farar hula ta Aung San Suu Kyi a shekarar 2021 Myanmar ta fada cikin rikici, an yi ta gudanar da zanga-zanga a yayin da ita kuma gwamnatin ta yi ta kokarin murkushe masu boren.