Shugaban Amirka Joe Biden yana cewa "Yanzu an yi adalci kuma wannan shugaban 'yan ta'adda ba ya raye. Mutane a duk faɗin duniya ba sa bukatar su ji tsoron mugun mai kisa. Amirka na ci gaba da nuna aniyarta da karfintana kare kasarta daga mugun iri. Muna sake nanata cewa, komin daren dadewa duk inda kuka buya, idan kuna barazana ga mutanenmu, Amirka za ta ganoku."
Me aka sani game da harin Amirka?
Dakarun Amirka sun kai harin ne a karshen mako, amma ta jinkirta fitar da bayanan har sai an tabbatar da mutuwarsa, kamar yadda jami'ai suka fada a ranar Litinin. Biden ya tabbatar da cewa aikin yaki da ta'addanci ya yi nasara kuma "babu farar hula da aka kashe." Ya ce ya amince da aikin a makon da ya gabata kuma an gudanar da shi a ranar Asabar.
A cewar shugaban na Amirka, al-Zawahiri ya koma Kabul ne domin haduwa da danginsa. "Babu daya daga cikin danginsa da ya ji rauni," in ji Biden.
Manyan jami'ai sun ce ficewar Amirka daga Afganistan a 2021 ya bai wa al-Qaeda damar sake samun karfi a Afganistan, ba tare da wani koma baya ba daga sabuwar gwamnatin Taliban. Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya nakalto wani jami'in leken asirin Amirka na cewa, gidan da al-Zawari yake a yayin harin mallakin babban mai taimaka wa babban shugaban Taliban Sirajuddin Haqqani ne.
Da alama wannan sabon harin zai dagula dangantakar da ke tsakanin Washington da Taliban.
Me jami'an Afghanistan suka ce?
A karshen mako dai da farko ma'aikatar harkokin cikin gida ta Taliban ta musanta rahotannin wani hari da jiragen yaki mara matuki suka kai a birnin Kabul. Sai dai kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya fada a safiyar yau Talata cewa jiragen yakin Amirka marasa matuka ne suka kai wani hari ta sama a wani gida da ke yankin Sherpur na babban birnin kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Taliban ta yi Allah-wadai da harin da Amurka ta kai, tana mai cewa ya kasance "karara ce ta keta ka'idojin kasa da kasa da kuma yarjejeniyar Doha." Sanarwar ta ce "Irin wadannan ayyuka maimaitawa ne na abubuwan da suka gaza a cikin shekaru 20 da suka gabata, kuma sun saba wa muradun Amirka da Afganistan da kuma yankin," in ji sanarwar.
Wanene Ayman al-Zawahiri?
An bayyana likitan fida dan kasar Masar a matsayin daya daga cikin wadanda suka kitsa harin da aka kai Amirka a ranar 11 ga watan Satumban 2001 wanda ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 3,000. An haifi shugaban al-Qaida ne a shekara ta 1951 ga wani fitaccen dangi mai daraja a Alkahira. Tun yana matashi, ya shiga haramtacciyar kungiyar 'yan uwa Musulmi. Yana cikin ɗaruruwan da aka kama aka kuma zarge shi da hannu a kisan shugaban kasar Masar Anwar Sadat a shekara ta 1981.
Duk da cewa an wanke shi daga tuhumar, ya shafe shekaru uku a gidan yari na Masar bisa zargin mallakar makamai - al'amarin da aka ce yana da kari. Ya tafi Afghanistan bayan an sake shi, inda ya san bin Laden kuma ya shiga yakin da aka yi da sojojin Soviet. An yi imanin Al-Zawahiri, ya kulla alaka mai karfi da bin Laden a karshen shekarun 1980, lokacin da ya yi jinyarsa a cikin kogo na Afghanistan, a lokacin da Tarayyar Soviet ta kai masa hari. Ya zama na biyu a shugaban al-Qaeda a 1998. Tun bayan kisan bin Laden da sojojin Amirka suka yi a 2011, al-Zawahiri ya kasance a cikin jerin wadanda hukumar leken asiri na Amirka FBI ke nema ruwa a jallo, inda suka ware kudi dala miliyan 25 a mastayin kudin lada ga dun wanda ya kwarmata bayanan inda yake.