Wannan mataki na gwamnatin Wahington ana ganinsa a mastayin wani yunkuri na karya tattalin arzikin Rasha kan mamaye Ukraine da take yi. Shugaba Joe Biden ya danganta karuwar takunkumin kai tsaye ga shaidun da ke nuna cewa sojojin Rasha sun kashe fararen hula da gangan a Bucha, wani gari da ke wajen Kyiv babban birnin kasar Ukraine.
Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Rasha tun da fari ta karyata zargin cewa ta aikata kisan gilla da gangan a garin Bucha, ta kuma kara da cewa zargin na iya rusa fatan da ake da shi na cimma yarjejeniyar zaman lafiya.