A ranar Juma'ar da ta gabata ne dai sojoji a Mali, suka ce sun kashe wasu da suka kira 'yan tawaye mutum sama da 200 a wani sintiri da suka kai yankin Moura mai fama da mayaka masu ikirarin jihadi.
Sai dai sanarwar sojojin ya zo ne daidai lokacin da wasu bayanai da aka yada ta kafafen sada zumunta suka zargi sojojin da kisan fararen hula masu yawa a yankin.
Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP da ya ruwaito wannan labarin, ya ce bai kai ga tantance sahihancin bayanan bangarorin biyu ba.
Ma'aikatar harkokin wajen na Amirka dai na ganin sojojin hayan nan na kamfanin Wagner da Mali ta dauko daga Rasha, su ne suka aikata kashe-kashen da ake batu a kai.