Amirka: Mai adawa da Trump ta fadi zabe

Amirka: Mai adawa da Trump ta fadi zabe
Trump, wanda ke son sake tsayawa takara a 2024, na kokarin ganin 'yan majalisar Republican 10 da suka goyi bayan zarginsa da hannu a kutsen majalisa, ba su sami tikitin jam'iyyar a zaben 'yan majalisa na Nuwamba ba.

'Yar majalisar Amirka Liz Cheney, ‘yar jam'iyyar Republican mai tsananin sukar Donald Trump, wadda ta goyi bayan binciken da majalisar dokokin kasar ta gudanar a kan mamayar ginin majalisa na Capitol, ta sha kaye a hannun wani dan takara da Trump ke mara wa baya a zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

Da take amincewa da kayen da ta sha, Cheney, ta ce duk da haka ba za ta sauya matsayarta a kan 'karerayin' da Trump ke ta yadawa a game da zaben Amirka na 2020 ba. Ta ce tsohon shugaban na yi wa salon mulkin dimukuradiyya barazana.

 


News Source:   DW (dw.com)