Amirka: Kotu ta daure mai barazanar kashe 'yan majalisa

Amirka: Kotu ta daure mai barazanar kashe 'yan majalisa
Mutumin ya amsa laifinsa a gaban kotu, na cewa ya tura sakonnin barazanar kashe 'yar majalisa Ilhan Omar daga jam'iyyar dimukurat da wasu 'yan majalisa mata guda uku.

Wani tsohon masoyin tsohon Shugaban Amirka Donald Trump, zai shafe shekaru uku a gidan yari tare da biyan tara har dala 7,000, abyan samunsa da laifin barazanar kashe 'yar majalisar wakilai Ilhan Omar da wasu mata 'yan majalisa.

Matashin mai suna David George Hannon, yana da shekaru 67, ya amsa laifinsa a watan Afril, inda ya ce ya aike da sakon barazana ta imel ga 'yan majalisun Democrat hudu bayan gudanar da wani taron labarai a watan Yuli 2019 don mayar da martani ga suka daga tsohon Shugaba Donald Trump, wanda ya ce ya kamata su "koma inda suka fito kuam inda da aka fi samun laifuffuka.


News Source:   DW (dw.com)