Tsohon shugaban Amirka Donald Trump ya ce jami'an hukumar bincike ta FBI sun kai wani samame a wani katafaren gidansa da ke bakin teku a jihar Florida, yana mai siffanta lamarin a matsayin rashin da'a. Hukumar ta FBI dai ta kauce wa yin karin haske a kan samamen. To amma Trump wanda ba ya cikin gidan a ranar Litinin da daddare, a cikin sanarwar da ya fitar ya gaza fadin dalilin da ya sa jami'an suka ziyarci gidansa suka kaddamar da bincike.
Jaridar New York Times ta ambato tsohon shugaban na zargin 'yan siyasar jam'iyya mai mulki ta Democrat da tura masa jami'an FBI domin su bankado wani abu da zummar goga masa kashin kaji, ya samu matsala, a takarar shugabancin Amirka da yake honkoro a shekara ta 2024.
A watan Fabrairun da ya gabata rahotanni sun ce an gano akwatuna 15 makare da muhimman takardun gwamnati da Mr. Trump ya wuce da su gidansa maimakon ya bar su a Fadar White House.