Ambaliyar ruwa ta halaka akalla mutane 21 a kudancin kasar Iran. Shugaban kungiyar bayar da agaji ta Red Cross a yankin Estahbah, Hossein Darvishi, ya ce akwai karin wasu mutane da ba a ji duriyarsu ba tun bayan da ambaliyar ruwan ta afku. A yayin da suke tabbatar da faruwar ifti'alin a wannan Asabar, hukumomin yankin sun ce tsakiyar lardin Estahbah ne ambaliyar ta fi yi wa ta'adi.
A shekara ta 2019, ambaliyar ruwa irin wannan ta yi ajalin mutum 76 a kudancin Iran sannan ta haddasa wa magidanta asarar da ta kai darajar kudi Dala miliyan 2000.