Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 148 a Nepal

'Yan sandan Nepal sun ce adadin mutanen ka iya zarce hakan kasancewar suna ci gaba da tattara alkaluma na mutanen da suka mutu daga mazauna karkara da ke gefen tsaunuka. An dai samu saukin isa wajen da ambaliyar ta yi barna sosai da masu aikin ceto ke kokarin kubutar da mutanen da ke da sauran numfashi.

Karin bayani: Girgizar kasa ta kashe mutane sama da 100 a kasar Nepal 

Galibi ana samun mamakon ruwan sama a yankin na Himalayan a watannin Yuni zuwa Satumba, to amma yanayin ya ta'azzara a wannan shekarar ta 2024 da masana ke cewa hakan na da nasaba da sauyin yanayi.

 

 


News Source:   DW (dw.com)