A cewar hukumomin kasar Chadi, ambaliyar ta biyo bayan ruwan sama da aka fara yi tun Juma'ar da ta gabata har izuwa jiya Laraba . Rahotanni suka ce ruwan da ya malala baya ga rayukan mutane 54 ya kuma share gidaje da yawa da kuma shaguna musamman a arewacin kasar ta Chadi. Shugaban ma'aikatar lura da yanayin kasar Idriss Abdallah Hassan, ya fada wa manama labarai cewa wannan ambaliyar ruwan ta shafi sauyin yanayi ne, wanda kuma ke faruwa kusan duk bayan shekaru biyar ko goma. Akasarin wadanda suka mutu sakamakon ambaliyar hadi da wadanda yanzu suka bace ana nemansu, baki 'yan ci-rani ne da ke aikin hako ma'adinai a lardin arewacin Chadi can kusa da iyakarsu da kasar Libiya.
News Source: DW (dw.com)