Ambaliya ta raba dubban mutane da gidaje a yammacin Afirka

Cikin wani rahoto da kungiyar agaji mai rajin kare hakkin kananan yara ta Save the Children, ta ce akwai mutum dubu 649 da 184 da suka rasa muhalli a Jamhuriyar Nijar sakamakon ambaliyar a bana.

Haka ma a Najeriya, ibtila'in ya shafi mutum dubu 225 sannan kasar Mali ta fuskanci ta'adin da ya shafi mutum dubu 73 da 780.

Sama da hektar gonaki dubu 115 da 265 su ma ruwan na sama ya lalata a daminar bana.

Yankunan na Afirka ta Yamma da suka fuskanci matsalar dai, sun fara gani ne daga cikin watan Yuni zuwa halin da ake ciki da ake ganin karuwar ruwan sama.


News Source:   DW (dw.com)