Adadin mutanen da suka halaka sakamakon ambaliyar ruwa a Afirka ta Kudu sun kai 440 kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar, yayin da masu aikin ceto ke kara kutsawa yankunan da aka samu iftila'in, yayin da ruwan saman da aka tafka ke raguwa.
Ruwan saman ya yi ta'adi a gidajen da ke birnin Durban da kewayensa yayin da mutanen yankin ke ci gaba da neman kai wa ga tudun mun tsira.
Hukumomin kasar ta Afirka ta Kudu sun tura daruruwan masu aikin ceto domin magance matsalolin da ambaliyar ruwan ta haifar.