Kasashen irin su Algeriya da Masar da Jordan da Libya da yankin Falasdinu har ma da Sudan da Tunisiya da wasu kasashe da ke bin mazhabar Sunni sun wayi gari da azumi a wannan rana ta Asabar 1 ga watan Maris 2025.
Karin bayani: A karshen mako Musulmai suka fara Azumi
Ministan kula da al'amuran da suka shafi addini a Indonesiya kuma kasar da ta fi yawan mabiya addinin Islama a duniya Nasaruddin Umar ya shaida ganin jinjirin watan a jiya Juma'a inda aka wayi gari da azumi a fadin kasar.
Karin bayani: Saudi Arebiya da makwabtanta na Gulf sun ga watan Ramadan
Morokko na daga cikin kasashen da ke bin mazhabar sunni da za a fara azumin Ramadana a ranar 2 ga watan Maris. Kazakila kasashen da ke bin mazhabar Shi'a irin su Iran suma zasu tashi da azumi a ranar Lahadi