'Yan bingida sun saba kai hare-hare a iyakokin Mali da Burkina Faso da kuma Nijar. Ko a ranar Talatar da ta gabata ma, 'yan ta'addan sun kashe wani mutum guda a Tillaberi tare da raunata wasu mutum uku kusa da garin Chatoumane, wanda daga bisani sojojin Nijar din suka maida martani ga ayyukan 'yan ta'addan.
Karin bayani: 'Yan bindiga sun kashe sojoji a yankin Tillaberi na Nijar
Sanarwar hukumomin Nijar ta ce 'yan ta'addan sun mayar da yankin Mehana a matsayin tungar masu ikrarin jihadi na IS da ke alaka da kungiyar Al-Qaeda a yakin Tallebri da ke kan iyakokin kasashen Mali da Burkina Faso.
Karin bayani: Nijar: Cece-kuce da UNDP kan binciken tsaro
Shugabannin mulkin sojin Nijar da suka karbi mulki a shekarar da ta gabata sun bayyana matsalar tsaro a matsayin dalilan hambarar da gwamnatin farar hula, amma wannan matsalar ta tsaro na ci gaba da kasancewa babban kalubale ga hukumomin kasar.