A wannan Talatar ne kasar Aljeriya ke bikinta na cika shekaru 60 da samun 'yancin kai daga turawan Faransa.
Albarkacin wannan ranar, gwamnati ta yi wa fursunoni dubu 14 ahuwa dama faretin soja na farko cikin shekaru da dama.
Tsohon shugaban Aljeriya Abdelaziz Bouteflika, ya yi watsi da duk wani fareti na soja, kafin Abdelmadjid Tebboune na yanzu ya waiwayi batun.
A ranar biyar ga watan Yulin shekara ta 1962 ne Aljeriyar ta samu 'yancin karkashin jagorancin wani mayakin sunkuru Ahmed Ben Bella, bayan kwashe shekaru bakwai ana yakin da ya yi sanadiyyar salwantar rayukan akalla mutum miliyan daya da dubu 500.
Aljeriyar dai ta kwashe shekaru 132 karkashin turawan mulkin mallakar.