Alhinin kisan 'yar jaridar Aljazeera

Alhinin kisan 'yar jaridar Aljazeera
Kafar watsa labarai ta Aljazeera ta dora alhakin kisan gillar da aka yi wa 'yar jarida Shireen Abu Akleh a yankin gabar yamma da kogin Jordan kan rundunar sojin Isra'ila.

Sa'o'i bayan kisan 'yar jarida Shireen Abu Akleh, shahararriyar kafar watsa labarai ta AlJeera da take yi wa aiki kafin ajalinta, ta dora alhakin kisan da ta kira na gilla kan rundunar sojojin Isra'ila.

Aljazeera ta fidda wannan sanarwar cike da alhini, bayan da bangaren Falasdinawa ya dora alhakin kisan gillar kan sojojin Isra'ila a yayin da sojin Isra'ila ke nuna yiwuwar Falasdinawa ne suka harbe ta a yayin da suke musayar wuta a tsakaninsu.

Shireen na kan aikin tattara rahoto a lokacin da ta gamu da ajalinta a safiyar wannan Laraba a gabar yamma da Kogin Jordan. Ta kwashi fiye da shekaru ashirin da biyar tana aikin aika wa aljazeera rahotanni, ta mutu tana da shekaru hamsin da daya a duniya. 
 


News Source:   DW (dw.com)