A wannan Jumma'ar alhazzai ke fita filin Arfa a ci gaba da aikin hajjin wannan shekara da maniyata fiye da miliyan daya da rabi daga sassa dabam-daban na duniya ke gudanarwa.
Bayan shafe daren jiya da aka soma shiga kololuwar aikin na hajjin bana a Mina, maniyatan za su shafe tsawon wunin yau suna ibada a dutsin Arafa, kafin kwana a Muzdalifa, wanda hakan ke daga cikin muhimman ranakun aikin hajjin.
Wannan ne dai karon farko da ake aikin hajjin cikin shekaru uku tun bayan bullar annobar Corona a fadin duniya. Aikin hajjin dai na daga cikin shika-shikan Musluncin da ya wajaba a kan kowane Musulmin da yake da gwargwadon hali na sauke faralin.