Alhaki ne ya kama shugaban Hezbollah da aka kashe - Biden

Shugaba Joe Biden na Amurka ya bayyana luguden wutan da ya halaka jagoran kungiyar Hezbollah a matsayin kamun alhakin wadanda Hassan Nasrallah ya kashe ne a baya.

Da safiyar Asabar ne Isra'ila ta ce ta kashe shugaban na Hezbollah a wani ruwan manyan makamai da ta yi wa kudancin Lebanon a ranar Juma'a, sai kuma daga bisani kungiyar ta tabbatar da mutuwar shugaban nata.

Karin bayani: Hezbollah ta tabbatar da kashe Hassan Nasrallah

Baya ga furucin nasa, shugaba Biden ya kuma umarci sakataren tsaron Amurka ya sake fasalce rundunoninta da ke Gabas ta Tsakiya domin jiran ko ta kwana, daga abinda wasu ke ganin yiwuwar barkewar yaki a yankin gaba dayansa.

A wani labarin kuma, gwamnatin ta Amurka ta umarci wasu daga cikin ma'aikatan ofishin jakadancinta da ke Beirut da kuma iyalansu su fice daga Lebanon, a yayin da ake kara zaman dar-dar a yankin na Gabas ta Tsakiya.

Karin bayani:Jamus ta yi kiran a dakatar da rikicin Isra'ila da Hezbollah

An kuma hana dukkan ma'aikatan ofishin jakadancin na Amurka tafiye-tafiye a cikin Lebanon ba tare da sahalewar gwamnatin Biden ba, a cewar wata sanarwa da ta fitar.


News Source:   DW (dw.com)