Jim kadan da kai harin Kungiyar al Shabaab ta fitar da wata sanarwa inda a ciki ta ce, ita ta kai wasu hare-haren bama-bamai kan wani sansanin sojin Kungiyar tarayyar Afirka da aka tsugunar a wani yankin mai suna Shabelle. Yanzu haka kungiyar mai gwagwarmaya da makamai ta ce, ta karbe ikon sansanin bayan artabun da ya biyo bayan gumurzun a tsakanin mayakanta dana rundunar AU da aka tsugunar a kasar don wanzar da zaman lafiya.
Wani ganau ya sheda wa kamfanin labarai na Reuters yadda karar fashewar bama-baman na safiyar wannan Talatar, suka tashi jama'a daga bacci tare da haifar da rudani. Al-Shabab dai ta shahara a kai hare-hare a sassan Mogadishu babban birnin kasar don nuna adawa da gwamnatin Somaliya dama sojojin wasu kasashen ketare da ke kokarin taimaka ma gwamnatin.