Ajentina ta fice daga WHO

Shugaba Javier Milei na kasar Ajentina ya ba da umurninn kasar ta dauki matakin ficewa daga cikin hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, saboda abin da ya kira sabanin da ke tsakanin manufofin gwamnatinsa da hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya.

Karin Bayani: BRICS: Ajantina ta yi watsi da tayin shiga

Asibiti a kasar AjentinaAsibiti a kasar AjentinaHoto: Julieta Ferrario/ZUMA Wire/imago

Mai magana da yawun fadar shugaban kasar ya tabbatar da haka a wannan Laraba, inda ake gani wani mataki na bin matakan Shugaba Donald Trump na Amurka, wanda yake dasawa da Shugaba Milei na kasar ta Ajentina. Hukumomin na Ajentina sun ce suna da sabani da hukumar saboda yadda ta tunkari annobar cutar Covid-19.

Wannan na zuwa lokacin da hukumar Lafiyar ta Duniya ta kaddamar da neman kudin taimako, bayan matakin janyewar kasar ta Amurka wadda take sahun gaba wajen bayar da kudin tafiyar da hukumar.

 


News Source:   DW (dw.com)