Afirka ta Tsakiya: Daina hukuncin kisa

Afirka ta Tsakiya: Daina hukuncin kisa
Kakakin majalisar wakilan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Simplice Mathieu Sarandji ya sanar da cewa, majalisar ta kada kuri'ar amincewa da haramta aiwatar da hukuncin kisa a kasar.

Rabon da a aiwatar da hukuncin kisa a kasar da yaki ya daidaita dai, tun a shekara ta 1981. Dokar dai za ta fara aiki ne kawai, bayan shugaban kasar Faustin-Archange Touadera ya sanya hannu a kanta. Tuni dai kungiyoyi masu rajin kare hakkin dan Adam ciki kuwa har da kungiyar kare hakkin dan Adam din ta kasa da kasa Amnesty International, suka bayyana matakin majalisar da abin maraba tare kuma da yin kira ga Shugaba Touadera da ya sanya hannu a kai. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar dai na zaman kasa ta baya-bayan nan a Afirka da ke son kawo karshen hukuncin kisa, bayan kasar Chadi da ta amince da daina aiwatar da hukuncin a shekara ta 2020 da kuma Saliyo da ta amince a shekarar da ta gabata ta 2021.


News Source:   DW (dw.com)