Afirka ta Kudu ta lashe gasar kwallon kafar mata ta nahiyar Afirka da aka kammala a ranar Asabar a kasar Moroko. Nasarar da matan Afirka ta Kudun suka samu ta biyo bayan kwallaye biyu da 'yar wasa Hildah Magaia ta jefa wa mai masaukin baki, Moroko, a cikin mintuna takwas bayan da aka koma hutun rabin lokacin.
Tawagar 'yan kwallon kafar ta matan Moroko ta yi duk kokarin da za ta yi na farke kwallayen da Afirka ta Kudun ta zura mata a raga, amma Morokon ta buge da tashi wasan da ci daya, duk da karin mintuna tara da aka yi a kan mintuna 90 na fafatawar mai zafi.
Wannan shi ne karon farko da matan na Afirka ta Kudu suka lashe kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka. 'Yan wasan Moroko su ma wannan shi ne karon farko da suka taba jiyo kamshin lashe kofin na mata, ta hanyar samun damar fafatawa da su a wasan karshe na gasar.