Afirka ta Kudu ta garkame iyakarta da Mozambique

Hukumar da ke kula da iyakokin Afirka ta Kudu ta sanar da cewa ta samu rahotannin kai wa wasu motoci farmaki a yankin gabar ruwa na Lebombo da ke kan iyakar kasar da Mozambique, wanda hakan ya sanya ta daukar wannan mataki domin dakile bazuwar tashin hankalin Mozambique zuwa cikin kasarta.

Karin bayani: 'Yan bindiga a Mozambik sun halaka manyan 'yan adawar gwamnati 

Matakin na zuwa a daidai lokacin da gamayyar jam'iyyun adawa suka kira zanga-zangar gama-gari a Alhamis 7 ga watan Nuwambar 2024, domin kalubalantar nasarar Daniel Chapo na jam'iyyar FRELIMO, wacce ta shafe shekaru da dama ta na sharafinta a siyasar kasar ta Mozambique.


News Source:   DW (dw.com)