Kasashen na G20 masu karfin tattalin arziki sun amince da shugabancin Afirka ta Kudu wacce kuma za ta jagoranci taron da kasashen zasu gudanar a nan gaba. Shugaba Ramaphosa ya ce wannan ne karon farko da Afirka zata karbi bakuncin taron na G20, inda ya ce zasu yi amfani wannan dama wajen tafiya da murya daya.
Karin bayani:An bude taron kungiyar G20 na bana
Da yake jawabi yayin karkare taron na birnin Rio de Janeiro, shugaban kasar Brazil mai masaukin baki Luiz Inacio Lula da Silva ya bukaci kaashen da ke gurbata muhalli dasu yi duk mai yiwuwa wajen cimma rage makamashin iskar da ke gurbata muhalli.