Afghanistan: Mutane da dama sun halaka

Afghanistan: Mutane da dama sun halaka
Rahotanni daga Afghanistan na nuni da cewa mutane da dama sun halaka, sakamakon wasu jerin hare-haren bama-bamai da aka kai a kan fararen hula.

Jerin hare-haren bama-baman dai, an kai su ne a Kabul babban birnin kasar da kuma gundumar Balkh da ke arewaci. Kakakin rundunar 'yan sandan birnin Kabul Khalid Zadran ya nunar da cewa, harin da aka kai a fadar gwamnatin Afghanistan din an kai shi ne a kan masallata a Masallacin Hazrat Zakarya da ke Kabul din. Mutane 22 ne dai wata kungiyar agajin gaggawa mai zaman kanta ta kasar Italiya ta bayaana cewa ta garzaya da su asibiti, sai dai daga cikinsu biyar sun halaka kafin a karasa da su asibitin. Haka kuma kimanin mutane tara ne suka halaka yayin da wasu 15 suka jikkata, a wasu jerin hare-haren da aka kai jim kadan bayan na Kabul din a birnin Mazar-e-Sharif kamar yadda kakakin 'yan sanda na gundumar Mohammad Asif Waziri ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus na dpa.


News Source:   DW (dw.com)