Cikin wata sanarda da ya fitar a Washington, mataimakin sakataren kudi na Amurka Wally Adeyemo ya ce takunkumin, wani yunkuri ne na tabbatar da alkawurran da shugaba Joe Biden da takwarorinsa na G7 suka yi na kawo cikas ga yunkurin Rasha na samar wa kanta da makaman da take yakan Ukarine da su. Wannan takunkumin karya tattalin arzikin ya shafi kamfanonin fasaha da wadanda ke hada-hadar kudi na Rasha.
Ma‘aikatar harkokin wajen Amurka na da niyyar mayar da hankali kan kamfanonin kasar Sin 15 da ake zargi da ci gaba da samar da kayayyakin ga masana'antun Rasha. Haka kuma ta sanar da rufe kofofin Amurka ga duk wadanda aka kakaba wa takunkumin.