Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gabatar da wasu daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan yarin Kuje a farkon watan Yulin da ya gabata.
A yayin da take nuna wa 'yan Najeriya fursunonin da ta yi nasarar sake kamowa, rundunar ta 'yan sandar, ta kuma gabatar da wasu masu garkuwa da mutane da fashin da makami da yawansu ya kai 21 a Abuja tare da makamansu. DSP Mustapha Bello Abdulkadir, wani jami'i a rundunar 'yan sandan Najeriyar ya shaida wa DW cewa sun samu wadanda ake zargin da miyagun makamai.
An dai kamo fursunonin da masu garkuwa da mutanen a jihohin Kaduna da Naija da Nasarawa da Filato da kuma Edo.