Abuja: Fursunoni 600 ne suka tsere daga Kuje

Abuja: Fursunoni 600 ne suka tsere daga Kuje
Ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta Najeriya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne suka kai harin domin kubutar da mambobinsu da ke tsare a gidan kason.

Kimanin fursunoni 600 ne suka tsere daga gidan yarin Kuje da ke Abuja, fadar mulkin Najeriya, bayan wani hari da ake zargin mayaka masu ikirarin jihadi da kaddamarwa. Sai dai kawo yanzu babban sakatare a ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar, Shuaib Belgore, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa sun yi nasarar kamo fursunoni 300 daga cikin 600 da suka tsere. 

Rahotanni sun ce lamarin ya faru a ranar Talata da daddare, inda mayakan suka yi amfani da abubuwa masu fashewa wurin fasa gidan yarin da ke kunshe da fursunonin da suka aikata muggan laifuka. 

A baya dai an sha samun irin wannan a Najeriya. To amma wannan shi ne karon farko da mahara suka fasa gidan yari a babban birnin kasar, Abuja.


News Source:   DW (dw.com)