Ababen fashewa sun tarwatse a Rasha

Ababen fashewa sun tarwatse a Rasha
Mazauna birnin Belgorod na kasar Rasha mai iyaka da Ukraine sun ce sun ji kararrakin ababen fashewa a safiyar Larabar nan. Gwamnan yankin ya ce kawo yanzu babu wani farar hula da lamarin ya jikkata.

Sai dai a farkon watan nan, Rasha ta zargi dakarun Ukraine da kai wa wata ma'adanarta ta man fetur hari a wannan birni. To amma can cikin Ukraine rahotannin da ke shigo mana yanzu haka na cewa, Rasha na can na ci gaba da barin wuta a gabashin Ukraine, inda tuni mazauna yankin suka fara gudun neman mafaka.


News Source:   DW (dw.com)