A Kashe fararan hula a Kwango

A Kashe fararan hula a Kwango
Akalla fararen hula 20 ne aka kashe a makon da ya gabata a garin Ituri da ke arewa maso gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyyar Kwango, a wani hari da ake dangantawa da na ‘yan tawayen ADF (Allied Democratic Forces).

Wani basarake yankin ya ce wani wanda ya shaida lamarin ya tabbatar masa da cewar ya ga gawarwakin mutane 30 a kwance a kauyen da lamarin ya faru na Monge da ke cikin lardin Ituri. Ituri da arewacin Kivu sun shafe shekara guda suna cikin wani hali na dokar ta baci amma har kawo yanzu an gaza samar da zaman lafiya a yankin. Inda kungiyoyin da ke dauke da makmai suka yi katutu fiye da shekaru 25, kungiya  ta baya-baya nan ita ce ADF ta masu yin jihadi

 


News Source:   DW (dw.com)