Alkaluma sun nunar da cewa jam'iyyar Alternative for Deutschland AfD) ta samu 30.5 zuwa 33.5% na kuri'un da aka kada yayin da CDU ta samu kashi 24.5% na kuri'un da aka kada a Thuringia. Sai dai a jihar Saxony, CDU ce ke kan gaba da 31.5 zuwa 32% yayin da AfD da ke kashi 30 zuwa 31.5% na kuri'un da aka kada.
Karin bayani: Jamus: An kawo karshen rikicin siyasar Thuringia
Wadannan tagwayen zabukan sun gudana ne mako guda bayan kashe mutane uku da wani dan Syria ya yi a garin Solingen, wanda ya girgiza kasar tare da sake farfado da muhawara kan shige da fice a Jamus.
Karin bayani:Zaben jihar ya dauki hankali a Jamus
Amma dai nasarar da AfD ta samu a Thuringia na zama na farko a kasar Jamus tun bayan yakin duniya na biyu, ko da yake manufofinta na wariya sun sa sauran jam'iyyun Jamus nesanta kansu da hada gwiwa da ita don kafa gwamnati a jihar.