A sanarwar hadin gwiwa da mahukuntan kasar Sudan ta Kudu gami da Majalisar Dinkin Duniya suka fidda a wannan Asabar ta nuna yadda sama da kaso 60 na cikin dari na al'ummar kasar ke cikin hali na 'yunwa da ke da nasaba da tashe-tashen hankula da kuma iftila'i da kasar ke fuskanta.
Kasar ta Sudan ta Kudu da ke zama jaririyar kasa ta jima tana fama da matsaloli tun bayan samun 'yancin a shekarar 2011, lamarin da ya kai ta ga kwashe tsawon shekaru a cikin yakin basasa. Majalisar Dinkin Duniya ta dora alhakin matsalolin da kasar ke fuskanta musamman ma na siyasa a kan shugaban kasar Salva Kiir da madugun adawa Riek Machar.