Zargin Cin Hanci: Zai Wuce, Zai Zama Labari - Amal

Zargin Cin Hanci: Zai Wuce, Zai Zama Labari - Amal

Tun bayan da labarin ya fantsama, abokan sana’arta da masoyanta suka yi ta wallafa sakon nuna alhini da yi mata fatan alheri.

Washington D.C. — 

Jarumar Kannywood, Amal Umar ta mika godiya ga abokan aikinta da masoyanta kan irin “soyayyar da aka nuna” mata bayan da wata kotu ta tuhume ta da laifin ba da cin hanci.

Amal, wacce tana daya daga cikin fitattun jarumai mata da ake damawa da su a masana’antar wacce ke arewacin Najeriya ta gurfana a gaban kotu a ranar Laraba kan zargin ba da cin hanci ga wani dan sanda.

“Ina cikin koshin lafiya, lafiyata kalau, kuma in sha Allah, wannan abin zai wuce, zai zama labari. Wannan na dauke shi ne a matsayin jarabawa.” Amal ta ce a wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram tare da jaruma Mansura Isah.

Tun bayan da labarin ya fantsama, abokan sana’arta da masoyanta suka yi ta wallafa sakon nuna alhini da yi mata fatan alheri.

Amal da Mansura Isah (Hoton bidiyo: Instagram/Amal Umar) Amal da Mansura Isah (Hoton bidiyo: Instagram/Amal Umar)

Shugaban Hukumar Fina-finai ta Najeriya kuma jarumi a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu ya yi kira ga jaruma Amal Umar da ta ci gaba da nuna juriya kan jarrabawar da take fuskanta.

“Ki ci gaba da juriya ‘yata,” Nuhu ya wallafa a shafinsa na Instagram.

“Allah ya ba ki mafita Amal Umar, rayuwa cike take da kalubale kala-kala. Allah ya datar da mu.” In ji Maryam Yahaya.

A zaman da ta yi a ranar Laraba, kotun ta tuhumi jarumar da ba da cin hancin Naira 250,000 ga ASP Salisu Bujama da ke Kano kan a murkushe wani binciken da ‘yan sandan ke yi kan wasu kudade Naira miliyan 40 da ake zargin saurayinta Ramadan Inuwa ya yi sama da fadi da su kamar yadda masu shigar da kara suka gabatar.

Amal a fim din "Nisan Dare" (Hoto: Instagram/ Amal Umar) Amal a fim din "Nisan Dare" (Hoto: Instagram/ Amal Umar)

Amal wacce tuni an ba da belinta bayan gurfana a gaban kotun ta musanta zargin ba da cin hancin.

Tun a watan Agustan 2022, Amal ta tsinci kanta cikin wannan cakwakiyar kudi ta Naira miliyan 40 inda ake zargin Inuwa (saurayinta) da barnatar da kudaden mallakin wani Yusuf Adamu.

A wancan lokacin, Amal ta amsa cewa Inuwa ya tura mata Naira miliyan takwas cikin asusunta, kodayake, rahotanni sun ce bincike ya nuna cewa kudaden da aka tura mata Naira miliyan 13 ne.

Tun a 2022, aka ba da belin Amal, amma an kwace wata mota da take hawa wacce ake zargin daga cikin kudaden ta saya.

Rahotanni sun ce Amal ta garzaya kotu ta nemi a hana ‘yan sandan ci gaba da gudanar da binciken, kotu kuma ta amsa mata amma a mataki na wucin gadi.

Amal a fim din "Don" (Hoto: Instagram/Amal Umar) Amal a fim din "Don" (Hoto: Instagram/Amal Umar)

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, hakan ya ba Amal dama ta bi sahun ‘yan sandan wajen kokarin ba su cin hanci don a yi watsi da karar baki daya.

Sai dai ‘yan sanda sun dakile yunkurin suka kuma kama ta suka gurfanar da ita a gaban kotun a karo na biyu kan zargin ba da cin hanci.

Jaruma Amal ta yi manyan fina-finai irinsu ‘Aliya’ da ‘Gidan Danja' da 'Nisan Dare' ta kan kuma fito a wakokin Hausa na zamani tare da manyan mawaka irinsu Umar M. Sharif da Lilin Baba.

Kazalika ta kan fito jifa-jifa a fina-finan harshen ingilishi kamar ‘Don’ da na masana'antar kudu ta Nollywood inda a baya-bayan nan ta bayyana a fim din da ake kira ‘Sugar.’

Tana kuma cikin sabon fim din da kamfanin 3 SP ke shirin sakewa da ake kira "Darasi."


News Source:   VOA (voahausa.com)