'Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Mawaki Rarara A Katsina

'Yan Bindiga Sun Sace Mahaifiyar Mawaki Rarara A Katsina

‘Yan bindiga dauke da muggan makamai sun yi garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar nan Dauda Adamu Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara.

'Yan bidigar sun yi garkuwa da Hajiya Halima a gidanta da ke garin Kahutu a Karamar Hukumar Danja ta Jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta tabbatar da labarin, inda ta rawaito cewa wasu majiyoyi daga kauyen sun ce da misalin karfe 1 na dare ranar Alhamis wayewar garin Juma’a ne maharan suka shiga gidan mahaifiyar Rarara suka dauke ta.

Majiyoyi sun ce 'yan bidigar a kafa suka zo, kuma ba su yi harbi ba a lokacin da suka kawo harin, wanda suka yi nasarar yin garkuwa da Hajiya Halima cikin ‘yan mintoci.

Lokacin da suke yunkurin tafiya da ita dattijuwar ba ta bijire mu su ba.

Duk da cewa ‘yan bindigar sun samu wasu mutane a gidan, amma mahaifiyar Rarara kadai suka dauka suka tafi da ita.

“Babu wani yunkuri da aka yi na tunkarar ‘yan bindigar a lokacin da suke tafiya da ita saboda suna dauke da bindigogi," in ji wani mazaunin garin.

Sai dai har zuwa yayin hada wannan rahoton ba’a ji ta bakin Rarara ba kan sace mahaifiyarsa.

Jihar Katsina dai na cikin jihohin da ke fama da matsalar masu garkuwa da mutane da satar dabbobi a cikin ‘yan shekarun baya-baya nan.


News Source:   VOA (voahausa.com)