Wutar Dajin California Ba Za Ta Shafi Bukukuwan Grammy Da Na Oscars Ba

Wutar Dajin California Ba Za Ta Shafi Bukukuwan Grammy Da Na Oscars Ba

Kamar yadda ake faɗa a masna’antar fina-finan Amurka ta Hollywood, dole ne Shirin ya ci gaba. A ranar Litinin, an ba da sanarwar cewa za a ci gaba da shirya bukukwan ba da lambar yabo na Grammys da Oscars kamar yadda aka tsara yi a ranar 2 ga Fabrairu da 2 ga watan Maris.

Washington,DC — 

Wannan sanarwa ta amsa tambayar da aka yi ta muhawara ta bayan fage ta masu zartar da hukunci da aka dorawa alhakin lalubo hanyar da za a shirya bukukuwan yayin da birnin Los Angeles ke fama da mummunar wutar daji.

Wasu fitattun taurari kamar Jean Smart da Patricia Arquette, sun yi kira da a dakatar da wadannan bukukuwan ba da lambar yabo ko kuma a sake fasalinsu ya zama wata hanyar tara kudi ta talabijin domin taimakawa yaki da wutar.

Kakar Bukukuwan Bada Lambar yabo Kakar Bukukuwan Bada Lambar yabo

Lokutan bukukuwan ba da kyauta kamar, Golden Globes, Grammys, SAG Awards, Oscars da sauran su - lokuta ne masu cike da nishadi a Hollywood.

Kallon taurarin da ake biya da kyau suna hawa dandamali suna karbar kyaututtuka yayin da dubban iyalai na Los Angeles ke gudun hijira kuma sun rasa gidajensu ka iya zama rashin tausayi.

Amma ta fuskar tattalin arziki, wadannan bukukuwa kuma suna ba da kudin shiga ga dubban ma'aikatan nishadi daga masu ba da abinci zuwa direbobi zuwa masu haska wuta, wadanda suke taka muhimmiyar rawa a masana'antar.

Bikin na Grammys shi ne ya fara sanar da cewa zai ci gaba da gudana duk da wutar dajin, amma bikin zai sake domin mayar da hankali a kan shawarar da wasu taurarin suka fara bayarwa kuma zai kara batun neman taimako.

Hoto Daga Bukin Grammys Hoto Daga Bukin Grammys

“A cikin wannan mawuyacin hali, waka za ta iya kawo waraka, natsuwa da kuma hadin kai,” in ji shugaban makarantar horar da mawaka, Harvey Mason Jr., kana shugaban hukumar amintattu Tammy Hurt shi ma ya fada a wata wasika a ranar Litinin cewa, “Bikin Grammys ba za ta karrama kwarewa ko nasarori a fanni waka kadai ba ne amma za ta kasance dandalin ba da kwarin gwiwa wurin jajircewa da ya sa birnin Los Angeles ta shahara.”

Wasikar ta ce za a ci gaba da bikin kamar yanda aka tsara tare da yin aiki da hukumomin yanki domin tabbatar da jama’a sun kasance cikin aminci da kuma yin amfani da albarkatun yankin ta yadda ya dace, kuma bikin zai zo da sabon salo.

Bikin zai kuma tara kudi don a taimakawa mutanen da wutar daji ta yi wa barna kana a karrama karfin zuciya da jajircewa da masu agajin farko suka nuna inda suka sadaukar da rayuwarsu domin kare namu.

Latin Grammy Latin Grammy

A makon da ya gabata, makarantar mawakan da sashen ba da tallafin na makarantar sun kaddamar da wani asusun tallafawa aikin kashe wutar, da dala miliyan 1 domin tallafawa mawaka da kwararru.

Yanzu da aka samu karin taimako, asusun ya raba sama da miliyan 2 na taimakon aikin gaggawa kuma zai ci gaba da wannan aiki.

Bikin Grammy dai shi ne babban shirin da za a nuna a talabijin nan gaba a ranar 2 ga watan Faburairu.


News Source:   VOA (voahausa.com)