Wizkid Ya Saki Waka Daga Kundinsa

Wizkid Ya Saki Waka Daga Kundinsa

Wizkid mai shekaru 34 ya kwatanta wannan kundi na “Marayo” a matsayin “mafi inganci” da ya taba yi a rayuwarsa.

Washington D.C. — 

Fitaccen mawakin Najeriya da ya taba lashe kyautar Grammy Wizkid ya saki waka mai taken “Piece of My Heart” daga cikin kundin wakokinsa da aka jima ana jira.

Wizkin wanda asalin sunansa Ayo Balogun ya yi wa kundin wakokin nasa taken “Marayo.”

Wakar da ta hada da fitaccen mawakin Amurka Brent Faiyaz.

“Piece of My Heart” ta dauki salon wakokin Afrobeat da kuma R&B.

Brent Faiyaz Brent Faiyaz

Kundin wakokin nasa mai taken “Marayo” na nufin “Ganin Abin Farin Ciki” da harshen Yarbanci.

An sake shi ne shekaru biyu bayan da Wizkid ya saki kundinsa na biyar “More Love, Less Ego.”

Wizkid mai shekaru 34 ya kwatanta wannan kundi na “Marayo” a matsayin “mafi inganci” da ya taba yi a rayuwarsa.


News Source:   VOA (voahausa.com)