Uwargidan Gwamnan Akwa Ibom Ta Rasu

Uwargidan Gwamnan Akwa Ibom Ta Rasu

Kwamishinan yada labaran jihar, Ini Ememobong, ne ya sanar da mutuwar uwargidan a sanarwar da ya fitar da safiyar yau Juma’a.

washington dc — 

Uwargidan gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, Patience Umo Eno, ta rasu.

Kwamishinan yada labaran jihar, Ini Ememobong, ne ya sanar da mutuwar uwargidan a sanarwar da ya fitar da safiyar yau Juma’a.

A cewar kwamishinan, uwargidan gwamnan ta mutu ne a asibiti a ranar 26 ga watan Satumbar da muke ciki, a kewaye da iyalanta.

Sanarwar mai taken, “cikin alhini muke sanar da da rasuwar uwargidan mai girma gwamnan jihar Akwa Ibom, Patience Umo Eno, sakamakon rashin lafiya.

“Ta mutu cikin lumana a asibiti a ranar 26 ga watan Satumbar da muke ciki, a kewaye da iyalinta.”

News Source:   VOA (voahausa.com)