Kente wanda ya samo asali daga al’ummomin Asante da Ewe na kasar Ghana, ya yi fice a duniya saboda dara-daran launukansa.
washington dc —Hukumar bunkasa tarihi da al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta shigar da sunan fitaccen tufafin Kente na kasar Ghana cikin jerin kayan tarihin dan adam.
Karbar da duniya ta yiwa Kente karkashin yarjejeniyar kasa da kasa ta 2003 akan alkinta kayayyakin tarihi ta kara fito da tasirin tufafin mai launuka da ake sakawa da hannu.
Kente wanda ya samo asali daga al’ummomin Asante da Ewe na kasar Ghana, ya yi fice a duniya saboda dara-daran launukansa.
Ministan yawon bude idanu Andrew Egyapa Mercer ya bayyana karramawar da Kente ya samu a matsayin wata shaida ta jajircewar Ghana wajen alkinta kayan tarihi da al’adu.
“Wannan nasara ta sanya Ghana a sahun gaba a kokarin duniya na alkintawa da mutunta al’adu,” a cewarsa.