Za’a sanar da tsare-tsaren jana’izarsa wata rana a nan gaba.
washington dc —Tsohon jarumin masana’antar shirya fina-finan Najeriya (Nollywood) Abdulsalam Sanyaolu, da aka fi sani da charles olumo ko “agbako” ya rasu yana da shekaru 101.
Shugaban kungiyar ‘yan wasan kwaikwayo da shirya fina-finai ta Najeriya (TAMPAN), Bolaji Amusan, da aka fi sani da Mr. Latin ne ya tabbatar da mutuwar agbako a sakon daya wallafa a shafinsa na instagram.
Mr. Latin yace za’a sanar da tsare-tsaren jana’izarsa wata rana a nan gaba.
“Tampan na sanar da rasuwar Pa Charles Olumo Sanyaolu, wanda ake yiwa lakabi da agbako. nan gaba kadan za’a sanar da tsare-tsaren jana’izarsa. Sai mun taho baba, daga 25/02/1923 zuwa 31/10/2024.”