Omori ya ba da umarni a daukan bidiyon wakoki sama da 200 ciki har da na fitattun mawakan Najeriya irinsu Davido, Fire Boy da Ashake.
Washington D.C. —Rahotanni a Najeriya na cewa fitaccen Darektan hada bidiyon wake-wake ThankGod Omori, wanda aka fi sani da TG Omori na kwance a asibiti yana fama da ciwon koda.
A wani sakon Twitter da ya wallafa a ranar Asabar, Omori ya ce daya daga cikin kodojinsa ta daina aiki.
“Shekara daya bayan da kodata guda daya ta daina aiki, an yi min dashen koda amma aikin bai yi ba.” Omori ya ce a shafinsa na X.
Ya kara da cewa, “dan uwana daya da nake da shi ya ba ni daya daga cikin nasa don na rayu.”
A cewar Omori, sau uku ana yi masa aiki kan wannan rashin lafiya.
A ‘yan kwanakin bayan ne Omori ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “ba na so na mutu.”
Omori ya ba da umarni a daukan bidiyon wakoki sama da 200 ciki har da na fitattun mawakan Najeriya irinsu Davido, Fire Boy da Ashake.