An dade ana yamadidin cewa Rarara da Humaira na soyayya inda aka rika hada hotunansu ana cewa suna shirin aure.
Washington D.C. —Fitaccen mawakin Hausa Dauda Kahutu Rarara ya ce alaka da ke tsakaninsa da jaruma Aisha Humaira ba wuce ta amince da yarda ba.
An dade ana yamadidin cewa Rarara da Humaira na soyayya inda aka rika hada hotunansu ana cewa suna shirin aure.
Amma yayin hirar da ya yi da Freedom Radio, Kano a shirin “Daga Kannywood,” Rarara ya ce babu batun soyayya a tsakaninsa da jarumar.
“Matsayin Aisha, ita ce ta uku a ofis dinmu (a mukami,) daga ni sai Aminu sai ita, babu wani abu da ya wuce wannan.
“Yadda take a jadawali na kamfani, musamman nawa, akwai aminci da yarda akwai kuma mu’amulla mai kyau.” In ji Rarara.
Ya kara da cewa, “ina fada zan kara maimaitawa, ita (Aisha) duk wanda yake mu’amulla da ita a industry (Kannywood) sai dai ya zalunce ta, ko da rigima ka ga ana yi da ita yawanci ita ce mai gaskiya. Kuma a ita ce mai gaskiyar za ta ce ta hakura. Duk wani furodusa ko darekta babu wanda zai ce maka ya taba fada da Aisha.”