Ranar 5 Ga Watan Mayun Badi Za A Fara Shari'ar Diddy

Ranar 5 Ga Watan Mayun Badi Za A Fara Shari'ar Diddy

Lauyoyin da ke wakiltar mawakin na hip-hop suna kokarin ganin an bayar da belinsa tun bayan kama shi da aka yi a ranar 16 ga Satumba.

Washington D.C. — 

An tsayar da 5 ga watan Mayun badi a matsayin ranar da za a fara sauraren karar da aka shigar da fitaccen mawakin Amurka Sean “Diddy” Combs.

Ana tuhumar Combs da laifukan da suka shafi safarar mutane don yin lalata.

An kai Combs kotun tarayya ta Manhattan daga gidan yari na Brooklyn don bayyana a gaban Alkali Arun Subramanian a ranar Alhamis da rana.

Mawakin ya musanta tuhume-tuhumen da suka hada da hadin baki wajen aikata muggan ayyuka da safarar mutane don yin lalata.

Lauyoyin da ke wakiltar mawakin na hip-hop suna kokarin ganin an bayar da belinsa tun bayan kama shi da aka yi a ranar 16 ga Satumba.

Sai dai Alkalin ya yanke hukuncin cewa idan aka ba da belin nasa zai iya zama barazana ga al’umma.

News Source:   VOA (voahausa.com)