Payne ya sha bayyanawa a bainar jama’a cewa yana fama da matsalar shan barasa, kuma ‘yan sanda sun samu rahoto akan “wani fusataccen mutum da ake zargin yana cikin mayen kwayoyi ko na barasa.”
washington dc —Mawakin nan dan asalin Burtaniya Liam Payne, kuma tsohon mamba a kungiyar samarin nan mai farin jini ta “One Direction” ya mutu a jiya Laraba yana da shekaru 31 da haihuwa bayan daya subuto daga hawa na 3 na benen wani otel a birnin Buenos Aires, a cewar ‘yan sanda da jami’an bada agajin gaggawa.
Sanarwar da ‘yan sanda suka fitar ta bayyana cewar “Liam Payne, marubucin waka kuma makadin jita, tsohon mamba a kungiyar mawaka ta “One Direction”, ya mutu a yau bayan daya fado daga hawa na 3 na benen wani otel.”
Shugaban hukumar ayyukan lafiya na gaggawa na Buenos Aires, Alberot Crescent, ya shaidawa wata tashar talabijin ta birnin cewar “babu sauran damar iya farfado da shi.”
Har yanzu ba’a iya tantance ko faduwar ta hatsari ce ba.
Payne ya sha bayyanawa a bainar jama’a cewa yana fama da matsalar shan barasa, kuma ‘yan sanda sun samu rahoto akan “wani fusataccen mutum da ake zargin yana cikin mayen kwayoyi ko na barasa.”