A yayin da ake ci gaba da nuna alhini ga mutuwar tsohon shugaban kasar Amurka Jimmy Carter, wanda ya rasu yana da shekara 100 a duniya
ABUJA, NIGERIA —Wasu masana siyasa da tsarin mulkin dimokuradiyya sun ce za’a dade ba’a sami zakakurin shugaba irin sa da ya koma rayuwar sa ta da, da ya yi kafin dandana mulki, sakamakon irin tasirin da ya yi a aikin kare kulla alakar diflomasiyya, hakkin bil’adama da dabbaka tsarin mulkin dimokuradiyya baya ga aikin noma.
Jimmy Carter Global DemocracyMutuwar tsohon shugaban kasar Amurka na 39, Jimmy Carter, mai shekaru 100 a duniya kuma wanda ya samu lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, ya sanya dubban mutane a kasashen duniya cikin alhini ganin irin tasirin da aka ce marigayin ya yi a fannin kulla alakar diflomasiyya, tabbatatar da zaman lafiya, kare hakkin bil’adama, noma da dai sauransu.
Tuni shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bi sahun shugabannin kasashen duniya wajen mika sakon ta’aziyya da nuna alhini ga rasuwar tsohon shugaban kasar Amurka, Jimmy Carter, baya ga gomman masana tarihi, siyasa, dimokuradiyya kasarsa da suka yi ta jajantawa kasar Amurka suna mai cewa an yi rashin zakakurin shugaba.
Najeriya dai na daya daga cikin kasashen nahiyar Afirka da marigayi Jimmy Carter ya ziyarta a lokacin da yake shugabanci a ranar 31 ga Maris zuwa 03 ga Afrilun shekarar 1978 a lokacin mulkin tsohon shugaba, Cif Olusegun Obasanjo.
Ko mene ne masana siyasa za su tuna da marigayi Jimmy Carter, Dakta Kichime Goyang Gotau, ya ce a iya sanin sa, ba bu irin shugaba Carter cikin shuwagabanni a kasashen duniya a yanzu.
Masanin tarihi kuma mawallafin jaridar Neptune Prime, Alhaji Hassan Gimba, ya ce zuwan marigayi Jimmy Carter Najeriya a shekarar 1978 na da muhimmanci matuka ba ga Najeriya kadai ba har da ita kan ta kasar Amurka don a lokacin, Amurka na neman karbuwa a nahiyar Afrika.
A cewar dattijon kasa mai shekaru 99 a duniya kuma jigo a siyasar Najeriya tun shekarar 1953, Alhaji Tanko Yakasai, ya bayyana cewa ko shakka babu zuwan Jimmy Carter ya daukaka darajar Najeriya a idon kasashen duniya.
Masana tarihi da siyasa da dama sun tabbatar da cewa ziyarar marigayi Jimmy Carter ya yi matukar tasiri ga daukaka darajar Najeriya sakamakon cewa shi ne shugaban kasar Amurka na farko da ya kawo ziyara Najeriya kuma daga bisani ya ziyarci Laberiya da kasar Habasha.
A lokacin da yake kan karagar mulki, marigayi Jimmy ya ziyarci nahiyoyi biyar da suka hada da Afirka, Asiya, Turai, Arewacin Amurka, da Kudancin Amurka.
Cikin ayyukan da marigayi Jimmy Carter ya yi har da na yaki da kwaro ga bangaren noma `11` da bin diddigin kuri’u a kasashe masu kananan karfi lamarin da ya kai shi ga samun kyautar Nobel ta zaman lafiya a shekara ta 2002, wanda ya biyo bayan cewa shi ne shugaba da ya cimma wata muhimmiyar yarjejeniyar zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, amma matsalolin tattalin arziki da kuma rikicin garkuwa da mutane na Iran suka yi masa cikas.
Saurari cikakken rahotannin Halima Abdulrauf kan marigayi Jimmy Carter:
Embed A Yada Marigayi Jimmy Carter Ya Kawo Sauyi A Duniya - Masana.mp3 by Muryar Amurka Embed A Yada The code has been copied to your clipboard. The URL has been copied to your clipboard Nuna wa mutane akan Facebook Nuna wa mutane akan TwitterNo media source currently available
0:00 6:00 0:00 Shiga Kai Tsaye 16 kbps | MP3 32 kbps | MP3 48 kbps | MP3 Bude sabon shafiMarigayi Carter Ya Kafa Tarihi A Zuwansa Najeriya:
Embed A Yada Marigayi Jimmy Carter Ya Kafa Tarihi A Zuwansa Najeriya.mp3 by Muryar Amurka Embed A Yada The code has been copied to your clipboard. The URL has been copied to your clipboard Nuna wa mutane akan Facebook Nuna wa mutane akan TwitterNo media source currently available
0:00 5:00 0:00 Shiga Kai Tsaye 16 kbps | MP3 32 kbps | MP3 48 kbps | MP3 Bude sabon shafiTarihin Zuwan Carter Najeriya Tare Da Hassan Gimba:
Embed A Yada Tarihin Zuwan Carter Najeriya Tare Da Hassan Gimba.mp3 by Muryar Amurka Embed A Yada The code has been copied to your clipboard. The URL has been copied to your clipboard Nuna wa mutane akan Facebook Nuna wa mutane akan TwitterNo media source currently available
0:00 3:16 0:00 Shiga Kai Tsaye 16 kbps | MP3 32 kbps | MP3 48 kbps | MP3 Bude sabon shafi