
Marigayi tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter, manomin gaydar da ya lashe zaben shugaban kasar Amurka bayan rikicin Watergate da yakin Vietnam ya mutu a watan Disamban 2024 yana da shekaru 100 a duniya.
Washington, DC. —Kafin mutuwar shi, an zabi Carter a jerin wadanda suka yi ayyukan da suka birge a rukunin littattafai cikin sauti, karatu da labari cikin sauti na kyautar Grammy na 2025 akan littafinsa mai taken “Last Sundays In Plains”: Wanda ya kunshi labarin shi na bukin cika shekaru 100,” da ya kunshi sautin muryar shi ta karshe na darussan da yake koyarwa na Sunday School a majami’ar Maranatha Baptist Church dake jihar Georgia.
Muryoyin mawaka irin su Darius Rucker, Lee Ann Rimes da Jon Batists sun kasance a cikin wannan sautin.
Wannan shine kyautar Grammy na 4 da Carter ya samu. Wannan kyautar da ya samu bayan mutuwar shi ya biyo bayan wasu kyautatuka 3 da ya samu a rukunin adabin baka.
Da tsohon shugaban ya lashe wannan kyautar kafin ya mutu, da ya kasance wanda ya lashe kyautar Grammy mafi yawan shekaru a tarihi.
Jikan Jimmy Carter Jason Carter, ne ya karbi kyautar a madadin shi. “Sarrafa (yin amfani) da kalmomin shi ta wannan hanyar abin a yaba ne ga iyalen shi da ma duniya baki daya,” abin da ya fada kenan a sa’adda yake gabatar da jawabin amincewa (godiya). “Ina godiya ga masanana”.
A wannan rukunin, Jimmy Carter ya doke Barbra Streisand, George Clinton, Dolly Parton da Frodusa Guy Oldfield.
Da a ce Streisand ce ta lashe kyautar ba Carter ba, da wannan ya kasance karon farko da ta taba lashe kyautar Grammy cikin shekaru 38.
A halin yanzu dai, mutumin da ya lashe kyautar ta Grammy da ya fi yawan shekaru a 2011 shine Pinetop Perkins mai shekaru 97.