Fitattun mawakan Najeriya da suka hada da Burna Boy, Davido, Tems, Ayra Starr, Olamide, da Asake, basu yi nasara ba a Kyautar Grammy ta 2024.
WASHINGTON DC —Duk da yake an sa sunansu a fannonin tantance mawakan da suka yi fice a wake-wake, ba su samu nasara ba a ko guda ba.
A rukunin makakin da ya fi fice a fannin kade kade da raye raye- sun sha kaye a hannun mawakiyar Afirka ta Kudu.
Mawakiyar Afirka ta Kudu ta doke su inda wakar ta “Water” ta zama waka mafi shahara a Afirka, a kundin Grammy din.
Burna Boy, wanda ya sami lambar yabo ta fitaccen mawaki a duniya na shekarar 2021, ya sha kashi a wannan karon a hannun Shakti. Mawakan Indiya sun yi nasara da wakar su "This Moment," inda suka doke Burna Boy da Davido.
Burna Boy ya zo a shirya domin yin daya daga cikin wakar shi da aka zaba a wurin bikin kai tsaye, sai dai bai samu yin hakan ba.