Kun san wanda ya kirkiri kalmar Kannywood?

Hakkin mallakar hotoINSTAGRAM/@OFFICIAL_HAFSAIDRIS20

Wani dan jarida kuma mai sharhi kan harkokin fina-finan Kannywood, Ibrahim Sheme, ya ce kalmar ta Kannywood wadda aka samar da ita a 2002, ta samo asali ne daga Malam Sunusi Shehu Daneji, wani marubucin Hausa a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Sheme ya shaida wa BBC cewa Malam Shehu ya fara amfani da kalmar ta Kannywood cikin wata mujalla mai bayar da labaran fina-finan Hausa, mai suna Tauraruwa.

A cewar Sheme, "ni ma na bayar da gudummawa wajen kirkiro wannan kalma, a lokacin da Malam Sunusi ya kirkiro wannan kalma yana amfani da 'N' guda daya a cikin kalmar Kanny din."

"Wato Kany ya rika amfani da ita. Da na ga yana amfani da kalmar Kannywood da 'N' guda daya, sai nake tunanin ba dai-dai ba ne," in ji Sheme.

Ya kara da cewa asalin kalmar daga Hollywood aka dauko ta sannan "masu yin harkar fina-finai na kudancin Najeriya suna amfani da Nollywood."

Sheme ya bayyana cewa a lokacin "na ga kamata ya yi a ce Kalliwood don haka sai na fara amfani da kalmar Kalliwood a cikin mujallar fim."

Ya ce a wancan lokacin shi Malam Shehu yana amfani da Kanywood da N guda daya sai dai daga baya ne kuma ya gane cewa mutane sun fi sabawa da kalmar da shi Malam Shehun ya kirkiro ta Kanywood.

Ya ce "don haka sai na koma amfani da Kannywood amma kuma sai na ki amfani da tasa a yadda yake rubuta ta."

"Sai na kara 'N' guda daya don ya zama Kannywood kamar yadda can yake Hollywood da Nollywood da 'L' guda biyu, toh sai naga ya kamata a rika amfani da N guda biyu." kamar yadda Sheme ya ce.

Tuni dai wannan kalma ta zama shahararriya a yanzu, ta yadda har aka sanya ta a kamus din Turanci na Oxford da ake wallafawa a Birtaniya a baya-bayan nan.


News Source:   www.bbc.com