Kannywood Na Jimamin Rasuwar Mahaifiyar Shamsu Dan Iya

Kannywood Na Jimamin Rasuwar Mahaifiyar Shamsu Dan Iya

Mahaifiyar jarumin ta rasu ne a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya a ranar Alhamis.

Washington D.C. — 

'Yan masana'atar Kannywood da ke arewacin Najeriya na ta mika sakon ta'aziyyarsu ga jarumi Shamsu Dan Iya wanda mahaifiyarsa ta rasu.

Mahaifiyar jarumin ta rasu ne a jihar Kaduna a ranar Alhamis.

“Inna lillahi wa’ainna ilahirraji’un, Allah ya yi wa mahaifiyata rasuwa yanzu. Jarumin ya wallafa a shafinsa na Instagram.

Tuni abokan sana’arsa suka yi ta taya jarumin jimamin mutuwar mahaifiyr tasa.

“Inna lillahi wa’ainna ilahirraji’un, Allah ya yi wa mahaifiyar Shamsu Dan Iya a garin Kaduna.” Shugaban Hukumar Fina-finai ta Najeriya kuma jarumi a masana’antar Ali Nuhu ya wallafa a shafinsa na Instagram.

“Allah ya jikanta, ya yi mata Rahama, Allah ya ba ku hakurin rashinta.” In ji jarumi kuma darekta Falalu Dorayi.

Shi kuwa jarumi Nuhu Abdullahi cewa ya yi, “Allah ya jikanta. Amin.”

“Allah ya jikan Mama da Rahama brother.” In ji mawaki kuma Jarumi Lilin Baba.

“Allah ya jikanta da Rahama.” In ji jaruma Hafsa Idris.

“Allah ya jikanta.” Mawaki Namenj ya ce.

Allah ya jikanta.” In ji Jaruma Teema Yola.

“Inna lillahi wa’ainna ilahirraji’un, Allah ubangiji ya jikanta da Rahama ya sa aljanna ce makomarta. In ji Umar M. Shariff.

“Allah ya mata Rahama.” In ji jaruma Maryam Booth.

Sai Jarumi Baballe Hayatu wanda shi ma ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Dan Iya kamar haka: “Inna lillahi wa’ainna ilahirraji’un, Allah ya jikanta. Ya sa mutuwa hutuce a gare ta. Allah ya sa ta je a sa'a...Ya sa aljanna makomar ta.”


News Source:   VOA (voahausa.com)